Colossians 1

1Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗanʼuwanmu.

2Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ʼyanʼuwa cikin Kiristi da suke a Kolossi:

Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu su kasance tare da ku.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da Uba da Ubangiji Yesu Kiristi


Adduʼar Godiya

3Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, saʼad da muke adduʼa dominku. 4Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege saʼad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6da ta zo muku. Koʼina a duniya wannan bishara tana hayayyafa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta. 7Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu, 8wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

9Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin adduʼa dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yǎ sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya: kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11Allah yǎ ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

Fifikon Kiristi

15Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16Ta wurinsa aka halicci dukan abu: abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyai ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yǎ zama mafifici. 19Gama Allah ya ji daɗi yǎ sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

21A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.

Hidimar Bulus ga Ikkilisiya

24Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato ikkilisiya. 25Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. 27Allah ya yi haka domin ya so ku Alʼummai ku gane abubuwan ban mamakinsa da kuma asirinsa mai ɗaukaka. Wannan asirin kuwa shi ne: Kiristi yana zama a cikinku, shi ne kuma begenku na samun rabo a cikin ɗaukakarsa.

28Saboda haka koʼina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi. 29Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.

Copyright information for HauSRK